Blatter: An bada hujja a tuhumar da ake masa

Wani mai kwarmata bayanai ya bada hujja a kan Sepp Blatter da ka iya taimakawa sosai a shari'ar ake masa

An haramtawa Blatter shiga harkar kwallon kafa har tsawon shekaru takwas saboda biyan wasu kudade na £1.3m ga Shugaban Uefa Michel Platini

Kuma lauyoyin Swiss na gudanar da bincike a kansa

An bayyanawa BBC cewa ofishin babban lauyan gwamnatin Swiss ya karbi bayanai masu amfani daga wani wanda ya bada shaida da ka iya taimakawa sosai

Ana zargin Blatter mai shekaru 79 a duniya da sanya hannu kan wani kwanturagi da ya sabawa Fifa

Blatter, wanda ya ke musanta ya yi ba dai-dai ba a lokuta da dama ya daukaka karra haramta masa yin kwallo.

Amma kwamitin da'a na Fifa na fatan a haramta masa shiga harkar kwallon kafar ma har iyakacin rayuwarsa