Kevin de Bruyne zai yi jinya

Hakkin mallakar hoto Getty

Dan wasan tsakiyar Manchester City Kevin de Bruyne ga alamu zai yi jinyar kusan makonni shida bayan ya samu rauni a gwiwarsa a wasan da suka yi nasara akan Everton a ranar Laraba

Dan wasan na Belgium mai shekaru 24 ya canza wasan bayan an taso shi daga benci amma ya fadi bayan an yi karin lokaci

Akwai fargabar cewa ba zai koma kwallo ba har karshen kakar wasannin

Sai dai ajen dinsa Patrick De Koster ya fadawa kafar yada labarai ta Sky cewa, Kevin ya fada min cewa abun da zai iya shine aiki tukuru domin ganin ya dawo murza leda

Ya kara da cewa Kevin ya na bakinciki. Burinsa shi ne taka leda. Ba zai buga wasu wasanni masu mahimmanci ba