'Ina tunanin raunin De Bruyne bai da tsanani'

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kevin de Bruyne ya nuna alamun zai dade yana jinya

Kocin Manchester City Manuel Pellegrini ya ce a tunaninsa Kevin de Bruyne zai ci gaba da murza leda kakar wasa ta bana, bayan da dan wasan ya ji rauni a wasansu da Everton.

Dan shekaru 24, shi ne ya kara musu tagomashi a wasan da suka doke Everton a gasar Capital One.

"Ina da kwarin gwiwa zai murza leda a bana," in ji Pellegrini.

De Bruyne ya zura kwallo daya a wasan da samu nasarar kai wa zagayen karshe.

A wata mai zuwa Manchester City za ta kara da Liverpool a wasan karshe a filin Wembley.