Abin takaici ne a ce zan yi murabus — Van Gaal

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ana rade radin makomar Kochin

Louis van Gaal ya bayyana labaran da ke nuna cewa ya yi tayin yin murabus a matsayin manajan Manchester United da cewa abin takaici ne

Wasanni uku kadai cikin wasanni sha ukun da Manchester United ta buga ne kadai ta sami nasara wadanda suka hada da gasar Premiya da FA Cup da Capital 1

Magoya baya sun yi wa Van Gaal da kuma 'yan wasan Manchester United ihu bayan da aka kammala wasan da Southampton ta ci su 1-0 a gida, abin da ya sake tayar da sabbin rade- radi game da makomar manajan

Van Gaal ya ce ''Wannan shi ne karo na uku da aka sallame ni kuma har yanzu ina nan."