Van Gaal: Za a iya kora ta idan har...

Hakkin mallakar hoto PA

Manajan Manchester United Louis Van Gaal ya ce za a iya korar sa idan har Derby ta doke su a gasar FA Cup a ranar Jumu'ah

Shugaban na Man United ya kuma bayyana rade- radin da ake yi cewar zai yi murabus bayan da Southampton ta ci su 1-0 da cewar abin takaici ne

Ya yi ikirarin cewar sau uku kafofin yada labarai suna korarsa a wannan kakar wasannin, amma ya ce ba za a iya doke su ba a gasar FA Cup a karo na hudu

Maiyiwuwa a lokacin za ku wallafa gaskiya saboda hakan na faruwa a cewar Van Gaal

Van Gaal ya kara da cewa hanyar da ake bi wajen yi masa tambayoyi game da makomarsa a kulob din ba ta dace ba

Mai horar da 'yan wasan mai shekaru 64 ya yi wa manema labarai jawabi ne a ranar Alhamis inda ya ce '' Kuna labaranku kuma mutane na yarda. Na damu cewa ana yarda da ku. Za ku iya rubuta duk abinda za ku iya''