Vidic ya yi ritaya daga murza leda

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Vidic ya dade yana jinya a Inter Milan

Tsohon kyaftin din Manchester United Nemanja Vidic ya sanar da yin ritaya daga buga tamaula.

Dan kasar Serbiya, ya lashe kofuna biyar na gasar Premier da kuma na zakarun Turai daya a cikin shekaru takwas da ya shafe a Old Trafford.

"Yawan jin rauni a cikin 'yan shekarun nan ne ya tilasta min yin ritaya," in ji Vidic.

Vidic mai shekaru 34, ya bar Inter Milan a cikin wannan watan na Janairu sakamakon yawan jin rauni.

Ya koma Inter Milan a watan Yulin 2014, daga Manchester United.