Wolfsburg na zawarcin Victor Osimhen

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sauran 'yan wasa daga cibiyar Ultimate Strikers su ma za a basu damar ziyartar Wolfsburg

Kulob din Wolfsburg na kasar Jamus ya amince da yarjejeniyar sayen dan wasan Nigeria, Victor Osimhen a shekarar 2017.

Dan wasan zai cika shekarau 18 ne a ranar 29 ga watan Disamba, saboda a karkashin dokar hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, dan wasan ba zai fara murza leda a matsayin kwararren dan kwallo ba sai ya cika shekaru 18.

Victor ya zura kwallaye 10 a gasar wasan kwallon kafa na 'yan kasa da shekaru 17 da aka kammala a watan Oktoba.

Abin da ya kai Najeriya ta dauki kofi a karo na biyar a gasar.

A karkashin yarjejeniyar da aka kulla tsakanin kulob din na Jamus da cibiyar koyar da 'yan kwallo ta Ultimate Strikers da ke Lagos a Najeriya, Victor ya ziyarci Wolfsburg kuma zai yi horo da su.