Tennis: Angelique ta taka wa Serena birki

Hakkin mallakar hoto no credit
Image caption Angelique ta dauki kofi

Yar wasan Jamus, Angelique Kerber ta hana Serena Williams ta dauki kofin a gasar Australian Open karo na 22.

Kerber, mai matsayi na bakwai a wasan na tenis ta lallasa Serena da ci 6 da 4 da 3 da 6 da kuma 6 da 4, a Melbourne Park.

Angelique, mai shekara 28 dai ta kasance 'yar kasar Jamus ta farko da za ta samu nasara a wasan mutum daya, tun shekarar 1999 lokacin da Steffi Graf ta samu irin wannan matsayi a gasar French Open.

Serena Williams dai mai shekara 31 ta fuskanci irin wannan kalubalen a karshen wasa karo na biyar ke nan, a gasa guda 26.

Yanzu haka, Kerber za ta zama mai matsayi na biyu a wasan tennis din.