FA Cup: Tottenham ta lallasa Colchester

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Yan wasan Tottenham suna murna

Kungiyar Tottenham ta lallasa Colchester, da ci 4 da 1, a gasar cin kofin hukumar kwallon kafa ta Ingila.

Dan wasan Tottenham, Nacer Chadli ne ya fara jefa kwallon farko a ragar Colchester kafin Eric Dier ya kara ta biyu.

Har wa yau, Chadlin dai ya kara ta uku sannan kuma dan wasan Colchester ya ci gidansa, shi kuma Tom Caroll ya jefa ta hudu.

Yanzu dai, Tottenham wadanda suka ci wasanni 10 a waje a gasar, ta samu damar shiga zagaye na biyar a karon farko tun 2012.