Everton na zawarcin Niasse

Hakkin mallakar hoto gett
Image caption Oumar Niasse

Kungiyar Everton ta na zawarcin dan wasan gaba na Lokomotiv Moscow, Oumar Niasse.

Ana sa ran karkare musayar dan wasan a kan kudi Fan miliyan 13.5 kafin ranar rufe musayar 'yan wasan da aka sanya waro Litinin.

Kociyan Everton, Roberto Martinez yana neman karin dan wasan gaba tun bayan fansar da Steven Naismith ga Norwich sannan kuma akwai yiwiwar Aiden McGeady shi ma ya tafi zuwa wani kulob din.

Shi dai Oumar Niasse wanda dan kasar Senegal ne ya zura kulob dinsa kwallaye 12 a wasanni 21, a wannan kakar wasannin.