Everton ta lallasa Carlisle Utd

Hakkin mallakar hoto PA

Everton ta samu nasarar buga zagaye na biyar na gasar cin kofin hukumar kwallon kafa ta Ingila wato FA Cup, bayan da ta doke kulob din Carlisle da ci 3 da nema, a filin wasa na Brunton Park.

Dan wasan Everton din, Kone ne ya fara daga ragar Carlisle a minti biyu da fara wasa.

Aaron Lennon ne ya jefa ta biyu bayan da Bryan Oviedo ya gara masa kwallon sannan Ross Barkley ne ya zarga ta uku a ragar Carlisle.

Wannan shi ne karo na biyar da da Everton din take zuwa zagaye na biyar na gasar ta FA.