CHAN 2016: Guinea ta kori Zambia

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan Guinea suna murna

Guinea ta samu nasarar ketara wa zuwa wasan kusa-da-na-karshe a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 'yan gida wato CHAN, bayan da doke Zambia da ci 4 da 5, a bugun fanareti.

Duk da cewa dukkannin bangarorin biyu suna da damar cin wasan amma sai a ka tashi ba ci.

Abdoul'aziz Keita ne dai ya raba gardama tsakanin kasashen bayan da ya zura kwallon ta biyar.

Yanzu Guinea za ta kara da Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo ne a wasan kusa-da-na-karshe ranar Laraba, a Kigali.