Musa ba zai je Leicester City ba

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ahmed Musa

Kungiyar CSKA Moscow wadda ita ce a saman teburin gasar league ta kasar Russia ta yi watsi da karin kudin da Leicester ta yi a kan Ahmed Musa, na Fan miliyan 18.7

A satin da ya gabata ne dai Leicester ta yi tayin Musa a kan kudi Fan miliyan 15.1.

CSKA dai ta ce suna son dan wasan nasu na gaba har zuwa karshen kaka.

Har wa yau, wasu manyan kungiyoyin Premier suna son sayen Ahmed Musa.