Newcastle na son sayen Berahino a kan £21m

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Saido Berahino ya ce ba zai sake komawa West Ham ba.

Kulob din Newcastle United yana son sayen dan wasan West Ham, Saido Berahino, a kan £21m.

Kociyan West Ham Tony Pulis ya ce Berahino, mai shekara 22, ya "bata watanni uku zuwa hudu" bayan an ki amincewa da tayin da Tottenham ya yi na sayensa a watan Agusta.

Dan wasan ya ce ba zai sake buga wa West Ham wasa ba sakamakon rashin jituwa tsakaninsa da shugaban kulob din Jeremy Peace.

Berahino ya yi fitowar ba-zata a wasan da suka kara da Peterborough na cin kofin FA ranar Asabar, kuma ya shi ne ya zura kwallaye biyu da suka tashi da ci 2-2.