Seydou zai koma Newcastle

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Seydou Doumbia

Kungiyar Newcastle ta fanshi dan wasan Roma, Seydou Doumbia.

Dan wasan mai shekara 28 dai zai taka wa Newcastle din wasa har zuwa karshen kakar wasannin nan, duk da cewa akwai yiwiwar mayar da kwantaragin na dun-dun-dun.

Shi dai Doumbia ya je Roma ne a watan Janairun 2015 a kan kudi Fam miliyan 10, sai dai kuma ya buga wasanni 13 ne kawai kafin daga bisani ya koma tsohon kulob dinsa na Locomotiv Moscow a watan Agusta.

Seydou Doumbia wanda ya ci wa Locomotive Moscow kwallaye 66 a wasanni 108, shi ne dan wasa na hudu da Newcastle ta rattaba hannu a kwantaraginsu a musayar 'yan wasa ta watan Janairu.