Olympics: BBC za ta watsa wasanni har zuwa 2024

Hakkin mallakar hoto google
Image caption Za a dai a yi wasannin ne na 2016 a Rio de Janeiro

Kafar watsa labaran BBC za ta rinka watsa labaran wasannin guje-guje da tsalle-tsalle wato Olympics guda biyar da za a gudanar daga yanzu har zuwa 2024.

Za dai a rinka watsa wasannin ne ta kafafen talbijin da radiyo da kuma intanet, a lokutan bazara da hunturu.

Yanzu haka BBC ta samu 'yancin watsa wasannin na shekarar 2016 da 2018 da 2020.

Sannan kuma ta hanyar hadin gwiwa da kamfanin Discovery Communications, kamfanin na BBC zai watsa wasannin da za a yi a lokacin huturu, a 2022, a Beijing da kuma wadanda za a yi a lokacin bazara a 2024.

Hakan dai na nufin cewa BBC za ta zama kamfanin da ya fi kowanne wajen watsa wasannin na Olympics ga masu sha'awar bibiya kyauta.

Za dai a yi wasannin Olympics din guda hudu masu zuwa a birane kamar haka: Rio de Janeiro(2016) da Pyeonchang(2018) da Tokyo(2020) da kuma Beijing(2022).

Sai dai kuma har yanzu ba a tantance birnin da za a gudanar da wasannin Olympics din na 2024 ba.