Cahil na son cigaba da zama a Chelsea

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Gary Cahill

Dan wasan baya na Chelsea, Gary Cahill ya ce ya yi tattauna da kociyan kulob din na rikon kwarya, Guus Hiddink sannan kuma yana son ya cigaba da taka wa Chelsea leda.

Gary, mai shekara 30 ya je Chelsea daga Bolton a watan Janairun 2012 sannan kuma ya sake rattaba hannu a kan wani sabon kwantaragin na shekara hudu a watan Disamba.

Sai dai kuma har yanzu bai taka leda ba a wasannin Premier tun zuwan nasa kulob din.

Shi dai Gary yana tsoron yanayin da zai iya tsintar kansa a ciki a gaba a kungiyar ta Chelsea.