An dakatar da 'yan wasan Nigeria daga buga wasa

Hakkin mallakar hoto
Image caption An samu 'yan wasan ne da laifin shan kwayoyin kara kuzari.

An dakatar da 'yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle na Najeriya takwas daga buga wasanni saboda an same su da laifin shan kwayoyin kara kuzari.

Hudu daga cikinsu sun lashe kyautar zinare a wasannin Afirka na shekarar da ta gabata, wanda aka yi a kasar Congo.

'Yan wasan da aka haramta wa shiga harkokin wasannin su ne:

  • Chinazom Amadi
  • Samson Idiata
  • Elisabeth Onua
  • Patience Opuene
  • Ebi James Igbadiwei
  • Deborah Odeyemi
  • Sunday Ezeh
  • Thomas Kure

An dakatar da dukkan 'yan wasan daga buga wasannin ne tsawon shekara hudu, idan ban da Elisabeth Onua, wacce aka dakatar daga buga wasanni tsawon shekara takwas saboda an same ta da laifin shan kwayoyin kara kuzari sau da dama.