Uche ya koma Malaga

Image caption Ikechukwu Uche

Dan wasan Najeriya, Ikechukwu Uche ya koma kulob din Malaga, watanni shida bayan da ya rattaba hannu a kan kwantaragi na shekara uku da kulob din Tigres UANL da ke Mexico.

Tun dai daga lokacin da Uche ya samu rauni a farkon wasansa a Tigres a inda kuma ya ci kwallo, ba a kara ganinsa ba.

Ikechukwu mai shekara 32 dai ya bar Villarreal ne a watan Yunin 2015.

Uche ya shaida wa BBC cewa " damar koma wa Sipaniya ta hanyar Malaga ta zo a lokacin da ya dace."

Dan wasan wanda dan Najeriya ne ya ciwa kasar tasa kwallaye 19 a wasanni 47.