Ranar bakin ciki a rayuwata -— Neville

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Gary Neville ya ce ba zai sauka daga mukaminsa ba.

Kociyan Valencia Gary Neville ya ce doke su da kungiyar Barcelona ta yi da ci 7-0 ita ce daya daga cikin ranakun da ya fi yin bakin ciki a rayuwarsa ta kwallon kafa.

A ranar Laraba ne dai suka sha wannan abin kungiyar a wasan kusa da na karshe na cin kofin Copa del Rey, kuma hakan ya kara kaimi ga masu sukar Neville, wanda bai ci ko da wasa daya cikin takwas din da ya jagoranta ba.

Neville ya ce,"Ba zan iya yin barci da daddare ba", ko da ya ke ya dage cewa ba zai sauka daga mukaminsa ba.

Ya kara da cewa,"Wannan shi ne babban bakin ciki da na fuskanta a rayuwata ta kwallon kafa."

Bayan kammala wasan ne dai, masu mu'amala da shafin Twitter suka kirkiro da wani maudu'i mai suna #Nevilleveteya, wato "Neville, ka sauka daga mukaminka" .

A watan Disamba ne aka nada Neville a matsayin kociyan kungiyar ta Valencia domin yin wa'adi daya.