Za a tuhumi Neymar da laifin almundahana

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Neymar ya sha musanta zarge-zargen da ake yi masa.

Masu shigar da kara a kasar Brazil sun bayar da shawarar a tuhumi dan wasan kwallon kafar kasar Neymar da laifuka guda hudu da suka danganci almundahana wajen biyan haraji kafin komawarsa kulob din Barcelona a shekarar 2013.

Ana zargin cewa an yi amfani da wasu kamfanoni ne a kan batun komawarsa Barcelona domin ya zillewa biyan haraji mai yawa.

Jami'ai a kasar ta Brazil sun ce zarge-zargen da ake yi wa Neymar kan zillewa biyan haraji sun kai shekara bakwai, tun daga shekarar 2006.

Wadannan tuhume-tuhume da ake yi wa dan wasan daban suke da wadanda ake yi masa a Spain, inda ya gurfana a gaban kotun Madrid ranar Talata.

Neymar ya gurfana a gaban kotun ne domin bayar da shaida a kan zargin cuwa-cuwa wajen biyan haraji game da komawarsa Barcelona.

Sai dai dan wasan ya sha musanta zarge-zargen.