Roger Federer zai yi jinyar wata daya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Roger Federer ne dan wasan da ya fi yin tashe a gasar Tennis ta Dubai.

Dan wasan kwallon Tennis na uku a duniya, Roger Federer, zai yi jinyar wata daya bayan an yi masa tiyata a gwiwarsa.

An yi wa dan wasan, mai shekara 34, wanda kuma sau 17 yana lashe manya manyan gasar na duniya, wato Grand Slam tiyata ne a kasarsa ta Switzerland.

Ya ji rauni ne kwana daya bayan ya sha kaye a hannun Novak Djokovic a wasan kusa da na karshe na gasar Australian Open a makon jiya.

Federer ya janye daga gasar Tennis ta duniya wacce za a yi a Rotterdam da kuma gasar cin kofin zakarun Tennis ta Dubai wacce za a yi a watan nan.

Shi ne dan wasan da ya fi yin tashe a gasar ta Dubai bayan da a bara, ya dauki kofinsa na bakwai a gasar, sannan ya lashe gasar Tennis ta Rotterdam sau biyu.