An haramta wa 'yan wasa wasa a Argentina

Image caption 'Yan wasa 15 aka haramtawa wasanni

Hukumar kwallon kafa ta Argentina ta haramta wa wasu 'yan wasa guda 15 buga wasa, sakamakon ba wa hammata iska da suka yi a lokacin wasan Estudiantes da Gimnasia La Plata.

'Yan wasan dai sun ta yi wa juna kulli da mahangurba al'amarin da ya janyo aka tsayar da wasan.

An dai haramta wa Alvaro Pereira da Mariano Andujar na Estudiantes tare da Nicolas Mazolla na kungiyar Gymnasia, buga wasanni guda takwas.

Sannan wasu 'yan wasan uku na Gimnasia su ma an hana su buga wasanni biyar.

Har wa yau, an dakatar da wasu 'yan wasa tara daga dukkan kungiyoyin daga buga wasa daga daya zuwa biyar. Kuma da ma gwamnatin Argentina ta haramta wa wasu 'yan wasan 12, shiga filayen wasanni har sai bayan an kammala wasannin league guda biyu.

Tuni dai dan wasan baya na Uruguay, Pereira ya bar kulob din na Estudiantes zuwa Getafe na La Liga har zuwa karshen kakar wasannin nan.