CHAN 2016: Mali ta doke Cote d'ivoire

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mali za ta kara da DR Congo a wasan karshe

Mali ta doke Cote d'ivoire da ci daya da nema, a wasan kusa-da-na-karshe na cin kofin nahiyar Afirka da ake yi a gida wato CHAN.

An dai kwashe tsawon lokaci ana kai ruwa rana tsakanin kasashen amma sai a dab da karshen wasan Mali ta jefa wa Cote d'ivoire kwallo dayar mai ban haushi.

Dan wasan Mali, Bissouma Yves ne ya ci kwallon.

Yanzu haka, Mali za ta fafata da Jamhuriyar Dimokradiyar Kongo a wasan karshe, ranar Lahadi. Yayin da ita kuma Cote d'ivoire za ta kara da Guinea a wasan neman matsayi na uku ranar Lahadi.