Celtic na komawa baya - Chris Sutton

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'yan kungiyar Celtic

Tsohon dan wasan Celtic Chris Sutton ya ce ya kamata ace kulob din ya sami sabon kociya kafin fara musayar 'yan wasa ta watan Janairu saboda kungiyar tana samun koma baya karkashin jagorancin Ronny Deila.

Sutton ya ce " Ana gane kwazon Celtic ne ta hanyar magoya bayanta da ke a nahiyar turai".

Ya ci gaba da cewa " a wannan kakar wasan, Celtic ta kunyata a turai. Ya kamata mu tambaya cewa ko akwai wani cigaba da aka samu a kulob din a tsawon watanni 12 da suka wuce? Ba bu. Celtic ba ta cigaba".

Cletic dai ba ta ji da dadi ba a hannun Aberdeen bayan da Aberdeen ta ci Celtic 2 da 1. Sannan kuma Ross County ma ta doke Celtic din wasan kusa-kusa-da-na-karshe na gasar Primier ta Scotland.

Sai dai kociyan na Celtic, Ronny Deila ya ce ba zai yi murabus daga kujerarsa ba.