Kenya ta lashe gasar tsere

Image caption Kasashe da yawa ne suka fafata a gasar

Dan wasan tseren fanfalaki na kasar Kenya, Abraham Kipton ne ya zama zakara a gasar tsaren fanfalaki na Marathon da aka yi a birnin Lagos da ke Najeriya.

Abraham ya lashe kyautar dala dubu 50, bayan da ya buge sauran abokan tseren nasa.

Shi dai Abraham tare da sauran masu tsere sun keta ta cikin birnin Lagos bayan da suka tashi daga babban filin wasa na birnin, suka kuma karkare a bakin teku.

Kimanin masu tsere 50 ne daga kasashen da suka hada da Eritrea da Ethiopia suka fafata a gasar.

Wannan dai shi ne karo na biyu da ake yin irin wannan gasar a birnin na Lagos, tun bayan na farko da aka gabatar a 1983.