PSG za ta gagari kungiyoyi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan wasan PSG

Kyaftin din Paris St-Germain,Thiago Silva ya ce mai yiwuwa ne kungiyar tasa za ta zama ta farko da za ta kai gaci a gasar League 1 ta Faransa, ba tare da an doke ta ba.

PSG din dai tana gab da sake daukar kofin karo na hudu a jere, bayan da ta doke Marseille da ci 2-1.

Yanzu dai kungiyar tana da maki 24 kuma ita ce a saman teburin gasar.

Silva ya ce " ina tunanin idan muka cigaba a haka, za mu iya kai wa karshen kakar wasannin ba tare da an doke mu ba."