Real Madrid sai ta tashi tsaye - Zidane

Hakkin mallakar hoto getty
Image caption Kociyan Real Madrid, Zinadine Zidane

Kociyan Real Madrid, Zinedine Zidane ya ce dole ne kungiyar tasa ta kara kaimi tun dai bayan wasansu da Granada a inda aka tashi 2-1.

Dan wasan kungiyar, Luka Modric ne ya samu ya jefa kwallo ta biyu a ragar Granada a minti 85.

Yanzu haka Real Madrid din tana mataki na 3 ne kuma akwai tazarar maki 4 tsakaninta da Barcelona.

Hakan ne ya sanya Zidane din fadin cewa " za mu yi kokarin gyara ko ina, bayanmu da gabanmu saboda muna bukatar zura karin kwallaye."