Bojan ya sabunta kwantaraginsa da Stoke

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Bojan dai ya taba buga wa kungiyoyin Roma, da Ajax, da kuma Milan wasa.

Dan wasan gaba na Stoke City Bojan Krkic ya saka hannu kan wata sabuwar kwantaragi da shekaru hudu da rabi da kulob din na ajin gwanaye.

Dan wasan mai shekaru 25 wanda ke buga wa kungiyar kwallon kafa ta kasar Spain wasa, ya je Stoke ne daga Barcelona a shekara ta 2014.

Bojan, wanda bai samu buga wasannin zagaye na biyu na zangon wasanni na bara ba saboda raunin da ya samu a gwiwa, ya ci wa Stoke kwallaye 10 a wasanni 41.

Shugaban kulob din Tony Scholes ya ce Bojan ya bayyana a fili cewa yanzu ya dauki kulob din na Stoke a zaman gida a gare shi.

Karin bayani