Johnson ba zai buga wasan Sunder da Man'U ba

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A inda aka fito dai dan wasan na tsakiya na buga wasa ne a kan beli.

Sunan Adam Johnson ba ya cikin jerin sunayen wadanda za su buga wa Sunderland wasa a karawar da za su yi da Manchester United ranar Assabar.

Johnson, dan shekaru 28, ya amsa laifin yin lalata da yarinya karama ranar Laraba.

Ana sa ran zai gurfana a gaban kotun Bradford Crown Court ranar Jumu'a kan zarge-zarge biyu na yin lalata.

Manajan Sunderland Sam Allardyce ne ya tabbatar da cewa bai saka sunan Johnson a cikin tawagar 'yan wasan nasa ba; a wajen wani taron 'yan jarida ranar Alhamis.

Karin bayani