"Mourinho ne kawai zai iya casa Guardiola"

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Benni McCarthy ya ce Guardiola ya sha kashi a hannun Mourinho sau da dama.

Tsohon dan wasan gaba na kungiyar Porto Benni McCarthy, ya ce Jose Mourinho shi ne kociyan da Manchester United za ta samu wanda zai iya kalubalantar Manchester City a kakar wasa mai zuwa.

BBC ta fahimci cewa tsohon kociyan na Chelsea yana tattaunawa da masu kungiyar United domin maye gurbin kociyanta Louis van Gaal a lokacin bazara.

McCarthy, mai shekara 38, ya taba murza leda a karkashin jagorancin Mourinho lokacin da yake kociyan Porto.

Ya shaida wa BBC cewa, "Mourinho yana daya daga cikin mutanen da suka san irin dabarun da Guardiola ke da su. A lokacin da Mourinho yake Real Madrid, ya doke Guardiola sau da dama. Haka ma a Inter Milan, ya yi galaba a kansa."

McCarthy ya kara da cewa a halin da ake ciki babu wani kociya da zai iya yin maganin Pep Guardiola idan ba Mourinho ba.

Tsohon kociyan Barcelona,Guardiola, wanda yanzu shi ne kociyan Bayern Munich, zai maye gurbin Manuel Pellegrini a matsayin kociyan City a bazara mai zuwa.