Fifa ta haramta wa Valcke shiga harkokin wasa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Fifa ta ce Jerome Valcke ya aikata laifuka da dama.

Hukumar kula da kwallon kafa ta duniya, Fifa, ta haramta wa tsohon Sakatare Janar dinta, Jerome Valcke, shiga dukkan harkokin wasanni tsawon shekara 12.

Fifa ta dauki wannan mataki ne bayan kwamitin da'arta ya same shi da laifi a game da sayar da tikitin gasar cin kofin duniya.

A lokacin da kwamitin ke yin bincike, ya bankado wasu laifuka na daban da Mista Valcke ya aikata, cikinsu har da cuwa-cuwa a kan kudin tafiye-tafiye da yin karan-tsaye ga dokokin hukumar.

Kazalika, an ci tarar Valcke, mai shekara 55, £70,800.

A watan Satumbar shekarar 2015 aka tilasta masa yin hutu, sannan aka kwace dukkan harkokin da ofishinsa ke gudanarwa daga gare shi har sai Illa Ma Sha Allahu sakamakon zarge-zargen badakalar da ake yi masa a lokacin.