Jackson Collision zai yi murabus

Image caption Jack Collision

Tsohon dan wasan West Ham United kuma dan wasan tsakiya na Wales, Jack Collision zai bar buga kwallo, saboda rauni a gwiwarsa.

Collision, mai shekara 27 ya buga wasanni ga West Ham har sau 121, sai dai kuma ya fuskanci matsalar ciwon gwiwa da ya samu a lokacin yana kulob din a 2009.

Bayan da ya bar West Ham, Collision ya rattaba hannu a wani kwantaragi da League one a Peterborough a 2015, kuma har ya buga wasanni 12.

Yanzu haka dai Jack Collision zai koma mai horas da 'yan wasa.