Man City ba ta ji dadin Tottenham ba

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Yan wasan Tottenham suna murna

Kungiyar Tottenham ta jefa kwallaye biyu a ragar Manchester City, bayan da dan wasan Tottenham, Christian Eriksen ya saka kwallon ta biyu ana dab da karkare wasa.

Harry Kane ne dai ya fara zarga kwallon farko a ragar ta Man City, kafin daga bisani Kelechi Iheanacho ya farke.

Yanzu haka, Tottenham din ce ta biyu a teburin gasar Premier da maki 51.

Kafin wasan da Tottenham da Man City suka buga, Arsenal ce ta kasance ta biyu a teburin na Premeir amma sakamakon Tottenham tafi Arsenal yawan kwallaye yasa ta shige gabanta.