Algeria: 'Yan wasa na shan kwaya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'yan wasan Algeria

Zarge-zargen shan kwaya a tsakanin 'yan wasan kasar Algeria ya jefa wasan kwallon kafar kasar cikin rudani, tun bayan dakatar da dan wasan kasar, Youcef Belaili da wasu manyan 'yan wasa uku daga buga wasa.

Kasar ta Algeriya dai ita kadai ce daga kasashen arewacin Afirka wadda ta fita zakka ta kuma buga gasar wasan kwallon kafa ta duniya ta 2014.

To amma sakamakon zarge-zargen shan kwayoyin na 'yan wasan kasar, ya sanya an fara dar-dar kan harkar wasan kwallon kafar Algeria.

Har wa yau, wani bincike da 'yan jaridu suka yi, ya nuna cewa akwai akwai matsalar rashawa da cin hanci a harkar wasan kwallon kafar kasar sakamakon rashin sanya ido.

Sai dai kuma, masu sharhi da masu sha'awar wasannin kwallon kafa na dora laifin ne a kan gwamnatin kasar da hukumar kwallon kafa ta kasar.