Joel Matip zai koma Liverpool

Image caption Joel Matip zai koma Liverpool

Dan wasan baya na Schalke, Joel Matip zai koma Liverpool a karshen kakar wasanni ta bana.

Schalke ta ce dan wasan mai shekara 24 zai koma Liverpool din ne da zarar kwantarinsa ya kare da kulob din na Jamus.

Matip wanda yake iya buga wasa a baya da gaba da ma tsakiya, ya fara buga wasa a gasar Bundesliga yana shekara 18 kuma ya buga wasanni sama da 200 a manyan kungiyoyi.

Joel Matip dai shi ne dan wasa na biyu da kociyan Liverpool, Jurgen Klopp ya nema tun bayan da ya zamo jagoran kungiyar, a watan Octoba.