Za a kwace kadarorin Neymar

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ana zargin Neymar da laifin zillewa biyan haraji.

Wata kotun tarayya da ke birnin Sao Paulo na kasar Brazil ta bayar da umarni a kwace kadarorin dan wasan kasar, Neymar, wadanda za su kai Dala miliyan hamsin.

Kadarorin sun hada da wani jirgin ruwa da jirgi mai saukar ungulu da kuma kayayyaki da dama.

Ana zargin Neymar ya laifin zille wa biyan haraji, kua yana fuskantar hukunci a kan batun.

Dan wasan na kungiyar kwallon kafar Barcelona ya musanta aikata ba daidai