Sunderland ta rage kudin sayar da tikiti

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Kungiyar Sunderland na dab da ficewa daga gasar Premier.

Kungiyar kwallon kafa ta Sunderland, wacce ake dab da fitarwa daga gasar Premier, ta rage kudin sayar da tikitin kallon wasa na shekarar 2016-17.

Kungiyar ita ce ta biyu a cikin rukunin kungiyoyin gasar Premier bayan West Ham ta dauki irin wannan mataki.

Shugaban kungiyar, Margaret Byrne, ta ce, "yana da kyau a rika sanya kudin sayen tikitin kallo ta yadda ba zai fi karfin 'yan kallo ba."

Kungiyar Liverpool ma ta dakatar da shirinta na sayar da tikiti a kan £77 a duk ranakun wasansu bayan masu goyon bayanta sun yi bore.

Yanzu dai Sunderland za ta rika sayar da tikitin da ya fi tsada a kan £59.