Chelsea na cikin tsaka-mai-wuya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Guus Hiddink ya ce har yanzu yana da kwarin gwiwa.

Kociyan Chelsea Guus Hiddink ya yi amanar cewa kungiyarsa tana da kashi hamsin cikin dari na kaiwa wasan dab da na kusa da karshe na gasar Zakarun Turai bayan Paris St-Germain ta doke su da ci 2-1.

John Mikel Obi ne ya farke kwallon da Zlatan Ibrahimovic na PSG ya zura musu, amma Edinson Cavani ya zura kwallo ta biyu.

Za su sake fafatawa a filin wasa na Stamford Bridge ranar tara ga watan Maris.

Hiddink ya ce, "Cin wasa a gidan wata kungiyar yana da matukar amfani. Ban ji dadin shan kayen da muka yi ba, amma ba wani abu ne da zai daga mana hankali ba."

Wannan ne karo na uku a jere da Chelsea ta kece-raini da PSG a gasar Zakarun Turai.

PSG ta yi nasara a irin wannan mataki a bara, bayan da Chelsea ta yi galaba a matakin dab da na kusa da karshe na kakar wasan shekarar 2014.