La Liga: Messi ya zura kwallo ta 300

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Lionel Messi ya fi kowa yawan kwallaye a La Liga

Dan wasan Bercelona, Lionel Messi ya zamo dan wasa na farko da ya jefa kwallaye 300 a gasar La Liga, bayan da ya zarga kwallaye biyu a ragar Sporting Gijon, a wasan da suka yi da yammacin Laraba.

Messi ne dai ya fara zura kwallon farko a ragar Sporting Gijon din wadda kuma ita ce kwallonsa ta 300 a gasar La Liga. Sai dai kuma Carlos Castro ya farke.

Lionel Messi ya kara ta biyu bayan da Luiz Suarez ya gara masa kwallon. Kuma Suarez shi ne ya zarga kwallo ta uku a ragar Sporting Gijon.

Yanzu haka Bercelona ce a saman tebur kuma akwai tazarar maki shida tsakaninta da Altico Madrid wadda ita take biye mata.