Europa: Rooney ba zai buga wasa ba

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wayne Rooney dai ya ci wa kulob din kwallaye 7 a wasanni 9 na baya bayan nan

Kyaftin din Manchester United, Wayne Rooney ba zai buga wa kulob din sa wasan farko na gasar Europa da FC Midtjylland na kasar Denmark, a ranar Alhamis.

A ranar Laraban nan ne dai ake sa ran kocin Manchester United din, Luis van Gaal zai yi bayani ga 'yan jarida dangane da dalilin da yasa Rooney ba zai buga wasan ba.

Shi dai Rooney ya ci kwallaye bakwai a wasanninsa tara na baya-bayan nan.

Manchester United ta shiga gasar ne a zagaye 32 na karshe, bayan da ta zamo mai mataki na uku a rukunun da take na gasar Champions League.