Nike ya raba-gari da Pacquiao a kan luwadi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Pacquiao ya ce littafin Linjila ya yi tur da masu auren jinsi daya.

Kamfanin da ke yin kayan sa wa na 'yan wasa, Nike, ya yanke dangantaka da Manny Pacquiao, bayan fitaccen dan damben zamani (boksin) din ya ce dabbobi ma sun fi masu aure jinsi daya.

Daga baya dai dan damben, mai shekara 37, wanda ke yin takarar kujerar majalisar dattawa a kasarsa ta Philippines, ya bayar da hakuri bisa kalaman nasa.

Sai dai a wata sanarwa da ya fitar Nike ya ce,"Kalaman Manny Pacquiao abubuwan kyama ne. Nike yana yin tur ga duk wanda zai nuna bambanci a tsakanin al'uma, kuma kamfanin ya dade yana goyon bayan 'yan luwadi da madigo."

Kamfanin ya kara da cewa: "daga yanzu babu wata dangantaka a tsakaninmu da Manny Pacquiao."

Pacquiao ya bayar da hakuri ne a wata hira da ya yi da wani gidan talabijin, ko da ya ke da farko ya kafe kan matsayinsa cewa "dabbobi sun fi masu auren jinsi daya daraja", yana mai cewa ya fadi gaskiya ne kamar yadda littafin Linjila ya bayyana.