Obafemi Martins zai koma wasa China

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Za a rufe kasuwar musayar 'yan wasa a China a ranar 26 ga watan Fabrairu

Tsohon dan wasan gaba na kungiyar Newcastle, Obafemi Martins ya zama tauraron dan kwallo na baya-bayan nan da zai koma taka leda a China.

Obafemi mai shekaru 31, zai bar kungiyar Seattle Sounders ta Amurka inda zai koma kungiyar Shanghai Greenland Shenhua ta China.

"Lokaci ya yi da zan fuskanci sabon kalubale a China, " in ji Obafemi yayin da yake bayyana komawarsa China.

Duka bangarorin biyu babu wanda ya tabbatar da tafiyar tasa, amma dan Najeriyan ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter.

Dan wasan ya bi sahun takwaransa na Senegal, Demba Ba, wanda ya koma kungiyar ta China.