Mun gamu da rashin sa a - Van Gaal

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Magoya bayan United ba su ji dadin wasan ba

Mai horar da 'yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Louis van Gaal ya bayyana rashin nasarar da kungiyarsa ta samu a karawarsu da Midtjylland a matsayin rashin sa a.

Dama can Van Gaal ba shi da 'yan wasa 13, sannan ya rasa David De Gea tun a farkon wasan, abin da ya sa kenan ya sadakar.

"Ina jin dama haka Allah ya kaddara," In ji Van Gaal.

"A mintoci 10 zuwa 15 na farkon wasan hankalin 'yan wasan na wani wuri, saboda haka ba muyi wasa sosai ba."

Sai dai Van Gaal na ganin daga baya 'yan wasan sun yi kokari ta yadda da za su iya kara zura kwallo.

Inda ya kara da cewa "Bayan an dawo hutun rabin lokaci, ba mu nuna kwazo ba, ba mu sake zura kwallo ba. Jesse Lingard ya samu damar zura kwallo har sau biyu."