Arsenal ta kasa doke Hull City

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Arsenal ce mai rike da kofin FA

Kungiyar wasa ta Arsenal ba ta zura wa Hull City kwallo ba a wasan da suka tashi canjaras wato kowa na neman ci, a gasar cin kofin FA Cup na hukumar kwallon kafar Ingila, a ranar Asabar, a filin wasa na Emirate.

Ya kamata dai ace Arsenal ta zura kwallaye akalla biyu sakamakon harin da 'yan wasanta Theo Walcott da Danny Welbeck suka kai ragar Hull City.

Shi dai mai tsaron ragar Hull City, Eldin Jakupovic ya kade kwallaye musamman wadda Joel Campell ya zargo a lokacin bugun tazara.

Arsenal dai ta dauki kofin FA har sau bakwai kuma idan ta dauki wannan zai zama na uku a jere. Ita kuwa Hull City ita ce mai kambun gasar Championship ta Ingila.

Yanzu haka, Arsenal za ta je gidan Hull domin sake karawa.