FIFA: Ba a sayen World Cup - Blatter

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Tsohon shugaban hukumar Fifa, Blatter ya shigar da koke kan dakatar da shi na shekara 8

Tsohon shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya wato FIFA, Sepp Blatter ya ce "ba abu ne mai yiwuwa ba a sayi karbar bakuncin gasar kwallon kafa ta duniya" wato World Cup.

Blatter mai shekara 79 yaki amince wa da tuhume-tuhumen da ake yi masa kan rashawa da cin hanci.

Ya fadi hakan ne a dai-dai lokacin da yake jiran sakamakon koken da ya shigar kan dakatar da shi da aka yi daga harkokin wasanni na shekara takwas.

Mista Blatter ya ce " na tabbata akwai adalci a duniya kuma ban aikata laifin da zai zama babban laifi ba."

Shi dai mista Blatter wanda ya kasance shugaban hukumar har karo biyar, an dakatar da shi daga harkokin wasa har na shekara 8 bisa zargin ba wa shugaban hukumar Uefa, Michel Platini cuwa-cuwar £1.3m.

A ranar 26 ga watan Fabrairu ne dai za a yi zaben shugaban FIFA.