Watford ta kai wasan dab da kusa da na karshe

Kungiyar kwallon kafa ta Watford ta kai wasan dab da kusa da na karshe a karon farko tun bayan shekarar 2007 sakamakon kwallon da dan wasan Leeds, Scott Wootton ya saka a cikin ragarsu .

Dan bayan ya yi kuskure ne lokacin da ya yi kokarin hana kwallon shiga cikin ragarsu.

Watford , wadda ta sauya 'yan wasanni shidda ta nuna kwazo sosai inda 'yan wasanta irinsu Miguel Britos da Almen Abdi sun dinga kokarin zira kwallo a cikin ragar Leeds.

Tun bayan shekara ta 2003 kungiyar Leeds ba ta sake shiga cikin kungiyoyin takwas na karshe a gasar cin kofin FA ba.