Ni ba mutumin kirki ba ne - Adam Johnson

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tsohon dan wasan Sunderland, Adam Johnson

Tsohon dan wasan Sunderland, Adam Johnson ya amince da cewa " bai kasance mutumin kirki ba ga budurwarsa ko kuma 'yarsa."

Ya tabbatar da haka ne a lokacin da yake bayar da shaida a gaban wata kotu a Bradford, bisa zargin yin lalata da yarinya.

Mista Johnson, mai shekara 28 ya yarda cewa ya simbaci yarinyar amma kuma yaki amincewa da wasu tuhume-tuhume guda biyu masu alaka da jima'i da yarinyar.

Ya kuma amince cewa ya aika wa wasu mata daban sakon wayar hannu.