Barcelona za ta bude kwaleji a Nigeria

Image caption Gwamnan Legas, Akinwumi Ambode da daya daga cikin hukumar gudanarwar Barcelona.

Kungiyar wasa ta Barcelona da ke Spaniya za ta kafa kwalejin horas da 'yan wasa a jihar Legas da ke kudu maso yammacin Nigeria, irinta ta farko, a Afirka.

Hakan ya bayyana ne a lokacin da hukumar gudanarwar kungiyar ta ziyarci gwamnan jihar ta Legas, Akinwunmi Ambode, a ofishinsa da ke Ikeja.

Gwamnan na Legas, mista Ambode ya ce ya yi matukar farin ciki da albishir din da hukumar gudanawar ta Barcelona ta kawo musu domin a cewarsa "babban cigaba ne ta fannin kwallon kafa."

Ya kara da cewa 'yan wasa irin su "Messi da Iniesta da Sergio Busquet da Pique duka sun fara daga irin wannan makarantar horaswar ce."