Bolton zai hade da Sport Shield Group

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Bolton Wanderers za ta hade da Sport Shield group

Kungiyar wasa ta Bolton Wanderers ta amince da ta hade da gamayyar kungiyoyin wasa ta Sport Shield group a kan £7.5, bisa yardar hukumar gasar Premeir League ta Ingila.

Hakan dai ya biyo bayan hukuncin da wata babbar kotu ta yanke na kungiyar ta biya harajin da ake bin ta daga yanzu zuwa 7 ga Maris.

An dai kammala rattaba hannu kan amincewa da hadewar kungiyar da Sport Shield group, tun kafin yanke hukuncin da kotun ta yi a ranar Litinin.

A watan Janairu ne dai kotun ta saurari karar cewa ana bin Bolton din harajin £2.2m.